Akwai wasu mazan zasu ga da sun soma neman aure komai na tafiya dai-dai sai daga baya suga wacce suke nema da aure ta sauya musu halayen da bai santa da su ba.
Hakan na faruwa ne saboda wasu munannan halayen da wasu mazan suke dasu idan mace ta auresu a hakan tana iya fuskantar matsala a zaman aurenta nan gaba. Don haka da ta hango hakan sai ta gwammace hakura da auren ta jira wani manemin.
Ga wasu halayen da suke iya jawo mace ta fasa auren namiji koda kuwa tana matukar son sa.
1: Rowa
2: Saurin Fushi
3: Rashin girmama iyayenta
4: Zagi ko duka
5: Rashin aikin yi
6: Wata matsala rashin lafiya
7: Karya
8: Rashin daukan alkawari da mahimmanci
9: Shaye-shaye
10: Rashin kula da addini
11: Zina ko Luwadi
12: Mu'amala da mutanen banza
Wadannan Abubuwan 12 da muka kawosu kowanne cikinsu na iya sa mace mai hankali da tunanin ta fasa auren namiji duk irin son da take masa. Domin kowanne cikinsu na iya nakasa mata zaman aurenta.
Da fatan matan zaku kula. Mazan kuma a gyara.