Domin Samari: Kafin Kayi aure a wannan loƙaci Ya kamata kasan da wannan abubuwan - Android Pols


A wannan lokacin samari da yawa suna daukin su yi aure ba tare da sun yi duba da wasu abubuwa da suke da muhimmanci a zamantakewar auren ba. 


Kwanon Shinkafa ƴar Hausa Naira 1800 Ne Gwangwani Man gyaɗa 250 Maggi ɗaya Naira 10 Biredi Wanda Mutum biyu za su iya Ci Naira 250 Taliya 450. 


Sabulun Wanka 200 Na Wanki 200 Kuɗin Ruwa Jarka ɗaya naira 50 a ƙalla ka sayi jarka biyu kullum naira ɗari.


Sai Ka Buga a sati ɗaya Kai da amarya da ƴan ƙannen amarya masu kawo ziyara za ku iya lashe Kwano Huɗu na shinkafa Kuɗinta Zai Kama naira 1850 ×4 Zai kama Naira 7400.


Biredi 250 a ƙalla ku siya sau biyar a sati Kuɗinka Zai Kama 1250.


Taliya a ƙalla ka sayi Guda Uku a satinnan kuɗinka zai kama 1350.


Kuɗin Ruwan sha na wanki dana wanka a ƙalla jarka biyu a rana naira ɗari sau 7 ya kama ɗari bakwai a sati.


Sabulun wanka da na wanki ,Maggi , Kayan Miya, Gas ko gawayi, Man girki Kuɗinsu zai Kama Naira 6000 A sati.


Shinkafar Sati Ɗaya - 7400

Biredi na Sati Ɗaya- 1250

Taliyar Sati Ɗaya-1350

Kuɗin Ruwa-700

Su kayan miya da sabulun wanka da wanki, gawayi ko Gas, Man girki -6000


Total ɗin Sati ɗaya duka 16,700

Total ɗin wata ɗaya-66,800


Wannan lissafi kada ka manta ba'a saka wasu abubuwa ba da yawa kamar kuɗin magani na rashin lafiya, kuɗin kayan kwalliya, auduga ta mata yayin Al'ada, Kuɗin taransifot na zuwa wajen aiki ko kasuwa na maigida, Ƴar madara ta watsawa a shayi, ɗan naman miya, gasu nan dai birjik.


Shi yasa Muke gayawa samari da babbar Murya idan baka samun a ƙalla dubu hamsin a wata ka haƙura da aure kaga dai lissafin dubu sittin ma tayi kaɗan, wannan kuma shine ƙarshen lissafi wanda ba kowacce mace ce zata iya yadda ta zauna a haka ba.


Da fatan samari za su yi duba da karatun ta nutsu kafin neman aure a wannan lokacin duba da yanayin rayuwa da hauhawar farashin kayan masarufi. 

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post