Kasancewar mu na ‘yan adam a doran ƙasa, Allah ya halicce mu ne don mu bauta masa kuma shi ne ya sanya soyayya da sha’awa a tsakaninmu.
Saboda haka samarin da suke ƙoƙarin ganin mallakan zuciyar ‘ya mace ko kuma samun zuciyarta ba tare da wata mishkila ba, ga wasu hanyoyin guda takwas da ake bi don sace zuciyar budurwa kamar haka :
1. TSARI: Duk wata ‘ya mace tana son ta ga namiji mai tsari, ba wai tsari irin na magana ba. Abin da nake nufi da haka shi ne, namiji ya kasance yana da tsarin rayuwa mai kyau, ba mutum ya zama shashasha maras kan gado ba.
2. KYAU DA KWALLIYA: Wasu matan suna son mutum mai kyau da kwalliya ba irin su wancan-nanka ba, sau da yawa za ka ga mata suna soyayya da saurayi saboda tsabar kyau da Allah ya ba shi, da kuma iya kwalliya kamar ɗawisu.
3. KALAMAI: Yana da kyau namiji ya zama ya iya kalaman da za su janyo hankalin duk wata ‘ya mace, rashin iya kalami kan janyo rashin masoyi. Maimakon haka sai ka zama tamkar ɗan bora a soyayya. Dole ne ka kasance ka iya kalaman da zaka birge budurwa.
4. KIRKI DA KULAWA: Namiji yakan tafiyar da zuciyar ya mace dalilin kasancewa mai kulawa da kirki. Misali duk bayan wani lokaci ko sa’ar da ba ta fi rana ɗaya ba, ko kwana biyu a ce kana zuwa ganin ta ko kuma kana kiran ta, idan ya yi yawa ne a ce kun haɗu sau uku. Musamman ma a irin wanan lokacin da wayar hannu ta zama ruwan dare. Wani lokacin idan haɗuwa ta yi ƙaranci sai ka kirata a waya.
Amma fa ka sani yawan zuwa gun mace ko masoyiyarka ce wani zubin nasa gundura. Ma’ana za ta ji duk ta gaji da ganin ka, musamman idan ya zama soyayyar taku ba ta yi ƙarfi ba.
5. KAR KA RIƘA YAWAN YI MATA MAGANA GABAN ƘAWAYE: Ka guji yawan kula yarinya cikin sahun ƙawayenta ko kuma cikin jama’a. Hakan zai karama kima, sannan da nesan ta kanka ga barin wulakanci. Wata kila lokacin da ka je mata cikin jama’a ko ƙawayen ta, ta ji tana son ka.
To amma watakila a lokacin shigar da ka yi bai yi mata ba. Hakan zai sa ta guje ka, wanda yin haka a soyayya wulakanci ne ga masoyi. Mafi kyawu shi ne ka jira ta keɓance ko kuma ta koma gida. Idan ba haka ba, to sai dai idan sun kai koda su biyar ne, to kuma ya zama dole ku kasance ku biyar koda sauran ba sa san ‘yan matan.
Saboda su kasance masu ɗauke masu hankali a lokacin da kuke hira kuma suma sauran ‘yan matan yin haka zai nuna cewa wadda kake so ba ta fita daban a cikin su ba. Duk abin da sauran ƙawayenta suka ce a kanka da shi za ta yi amfani.
6. BARKWANCI: Idan ka kasance mai raha ga masoyiyarka to nan da nan za ka sace zuciyarta. Misali ka riƙa ce mata a duk lokacin da ka zo hira da ita, amincin so gareki ya tauraruwan zuciyata, ɗaya tamkar da goma cikin sahun mataye, ado da kyau siffarki ce, murmushinki ke sanya zukata fara’a. gimbiya adon ‘yan mata. Da sauran su.
Kana mai ambaton haka cikin murmushi da shauƙi irin na soyaya kuma dole ne hirarku ta kasance mai amfani ba ka yi ta zuba ba, har sai ka gundure ta. Yawan magana ba shi da tasiri a soyayya muddin ba magana ne masu ɗauke hankali da san ji ko rashin gundura ba.
7. KUƊI DA KULAWA: Mata suna son samun saurayi mai tashen kudi da kulawa cikin bukatunsu a koyaushe. Idan ta samu wanda ya haɗa waɗannan abubuwa kuma ya tafiyar da su yadda ya kamata, to abu ne mai sauƙi ya sace zuciyar budurwa. Akwai mazan da suke roƙon ‘yan matansu kuɗi; wannan ba soyayya ba ce, sai a kira shi a kwaɗayi.
8. KYAUTATAWA: Sai dai kuma duk da na yi bayani kan cewa kwaɗayi bashi da kyau a soyayya, hakan ba shi yake nuna ba za ka kyautatawa masoyiyarka ba. Hasali ma idan kai haka, to za ka ƙara ƙarfin shaƙuwa ne tsakanin ku da juna.
Sai dai idan za a yi kyauta duba me masoyiya take da buƙata a daidai wannan lokaci. Misali, kar ka kawo mata hoda a lokacin da take buƙatar turare, atamfa, yayin da ita kuma leshi take so. Sanin haƙiƙanin abin da budurwa ke so, ko da ku fara soyayya da ita, ko ba ku fara ba, yana taimakawa ƙwarai wajen sace zuciyarta.
Dr-Nuraddeen katsina