Domin Mata: Hadin Man Gyaran Gashi (Baki Da Laushi) - Android Pols - Android Pols - latest news, natural remedies, and entertainment

Domin Mata: Hadin Man Gyaran Gashi (Baki Da Laushi) - Android Pols


Wannan kuma man gashi ne mai sa laushin gashi da tsawo ya yi baki yana shekin haske.


Wannan hadin ba zai taba barin gashin ki ya kare-raye ba kuma zai rika laushi sosai da tsayi. 


Da farko zaki tanadi:


1. Zaitun shitta

2. Man alayyadi

3. Man zaitun

4. Man kwakwa

5. Man albasa

6. Man hulba

7. Man ridi


Za ku hada hulba da lalle waje daya sai ku tafasa, sannan sai ku tace ku wanke kai da shi, sannan ku hade dukan wannan mayuka da na lissafo ku rinka shafawa a kan ku za ku ga gashin ku yana kara kyau.


Da fatan Idan kuna jarraba kunga yai muku aiki za ku yi kokarin sanarwa da sauran 'yan uwa mata. 

Related Posts:
Previous article
Next article

Leave Comments

Post a Comment

Iklan Atas Artikel

Iklan Tengah Artikel 1

Iklan Tengah Artikel 2

Iklan Bawah Artikel