Domin Ma'aurata: Shawarwari Domin Samun Gamsuwa Da Jindadi A Yayin Kwanciyar Jima'i - Android Pols



Akwai abubuwan da ya kamata ma'aurata su rika kiyayewa a yayin mu'amalar aure, sai dai ba duka ma'aurata ne ke kulawa ba. Hakan yasa muka kawo muku wasu shawarwari da za su amfane ku. Ga su kamar haka :


1. Idan kana son jin dadin jima'i karka rika yawaita shan maganin karin karfin maza, Musamman na kwayoyi.


2. Karka rika koyi da masu video na jima'i (blue film) wajen cewa sai kayi yadda suke yi. Kai dai kawai yi kokarin yadda za ka gamsar da matarka ba tare da da ka takura kanka ba. 


3. Karka rika kusantar matarka lokacin da ba ta son Jima'i, kuma ta nuna maka haka, sai kace yi hakuri ko da iya wasannine ta yi maka don ka samu gamsuwa. 


4. Yi kokarin gano abubuwan da matarka take so ko tafi jindadin ka yi mata wasa dasu idan ana wasannin sunna. Domin wasu matan Kunya kan hanasu bayyanawa mijinsu abinda suka fi so a taba musu ko kuma a tsotsar musu. 


5. Kai da matarka ku rika yawaita shan kayan marmari, kamar su ayaba lemo da kankana domin suna taimakawa sosai wajen kara inganta lafiya da kuma sha'awa. 


6. Ku rika motsa jiki koya yake, sannan ku rika kokarin samun hutu da bacci sosai, domin hakan na kara lafiyar jiki da samun kwanciyar hankali. 


7. Kar kayi Jima'i lokacin da baka da cikakkiyar sha'awa, domin ba za ka samu gamsuwa ba.


8. Idan dayan ku yana da wata cuta, bangaren lafiya a yi kokari a magance wannan matsala kafin a cigaba da jima'i.


9. Karka kusanci iyalin ka lokacin da take al'ada ko ciwon mara. Ka yi hakuri har sai lokacin da ta samu lafiya. 


10. Ka Rika kyautata muamalar ka tsakanin ka da iyalin ka, sannan kayi kokarin kamanta adalci.


Wannan sune abubuwa 10 da ya kamata duk ma'aurata su rika kiyaye dasu a zamantakewar aurensu, babu shakka Indai an bi wadannan shawarwari da muka bayyana za'a ji dadin zama cikin lafiya da kwanciyar hankali, Allah yasa mu dace.


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post