Akwai wasu dabi'u da halaye na wasu mazan da suke cutar da mata dasu. Wasu mazan kuwa suke zubarwa kansu mutunci dasu. Akwai mazan da suke rasa soyayyar da ake yi musu saboda su.
Duk namijin da yake son yayi kyankyawan mu'amala da mace musamman wacce yake nema da aure ko wacce ya aura. To wajibi ne ka guji yiwa mata wadannan abubuwan kamar haka:
1: Kada Ka Furtawa Mace Kalmar So Bada gaske kake ba. Domin su mata suna da saurin yadda da kalmar so duk wanda ya furta musu suna zaton hakan dagaske ne.
2: Duk Munin Mace Kada Kace Mata Mummunace Ita. Babban abinda mace ta tsana a duniya shines a ce ba ta da kyau ita mummuna ce, duk irin yadda kuke wasa da mace ka kiyayi furta hakan gareta.
3: Kada ka sake ka kwatanta mace da wata muddin ba cewa za kayi ta fita da wani abun ba. Duk mace ba ta san a hada ta da wata ita tafi son koda yaushe ace ita ce kan gaba.
4: Kada Ka yiwa mace tsawa. Duk irin yadda ka kai ga mace ka guji hantararta da yaimata tsawa.
5: Kada ka sake ka tona wani sirrin da mace ta baka ko ta fadamaka. Mata suna son sirri kuma suna son idan sun yadda dakai su sanar dakai dukkan damuwarsu amma bayyana sirrin su ga wani basa so.
6: Kada ka yiwa mace alkawarin da ba za ka cika ba. Mata suna saka abu a ransu idan aka yi musu alkawri, idan har kasan back za ka iya cika wannan alkawrin ba kada ka yi wa mace.
7: Kada ka ci amanarta musamman da wata na kusa da ita.
8: Kada ka gwaleta a cikin mutane ko yi mata gyara na kaskanci.
9: Kada cutar da ita saboda soyayyar da take yi maka.
10: Kada ka zama mai tsautsauran ra'ayi ko akida akanta.
Mace idan tana yinka, tana yinka ne gaba dayanta jini da tsoka, ranta da mutuwa. Don haka amfani da wannan nakasar kada ya baka damar ka cutar da ita.
Kada ka sake ka yiwa macen da take sonka abinda ba za ka so a yiwa ta kusa da kai ba, su mata mutanen mu ne.