Zakaran da Kotu ta yankewa hukuncin Yan Kashi a ranar Good Friday, maishi ya zartar da hukuncinsa.
Mutumin da ya mallaki zakaran da aka zartar wa hukuncin kisa a jihar Kano, ya ce bai ji daɗin yadda marigayin ya haɗa shi faɗa da maƙwabcinsa ba.
A ranar Talatar da ta gabata ne, Mai shari’a Halima Wali a wata kotu da ke Kano ta yanke wa zakaran hukuncin kisa
Matakin ya zo ne bayan wasu maƙwabtan mai zakaran biyu suka shigar da ƙara, inda suka zargi zakaran da hana su sakat saboda yawan cara, da zarar sanyin asuba ya kaɗa.