Hukumar yan sanda a Nijeriya ta kori wasu jami'anta uku dake tsaron mawaƙin siyasa, Dauda Kahutu Rarara, bisa samunsu da laifin karya dokar aiki na harbi ba bisa ƙa'ida ba.
'Yan sandan da aka sallama daga aikin su ne, Insp Dahiru Shu'aibu, Sgt Abdullahi Badamasi da Sgt Isah Danladi kamar yadda mai magana da yawun rundunar 'yan sanda ta kasa Olumuyiwa Adejobi ya sanar.
Ya kuke ganin wannan matakin na rundunar yan sanda, kuna ganin hakan ya dace?