Abubuwan Da Matan Aure Ke Yiwa Mazajensu Da Ake Zato Asiri Ne - Android Pols


Mun tattauna da wasu mata da suka bayyana mana abubuwan da suke yiwa mazajensu wanda duk inda miji ya tafi hankalinsu yana kan matarsa zai yi kokari ya dawo gareta. 


Wata mata tace, idan zan tashi mijina daga bacci dan yai sallah sai na wanke hannuna da ruwan sanyi, na shafa turaren da yafi so a hannu na, sai in shafi dumin jikin shi in kai hannu na kusa da hancin shi. Wannan kamshin turaren sai ya sanya ya farka daga baccin shi koda ko ya kai kololuwa a bacci da minshari mai karfi. Kuma hakan na sa shi yayi gaggawan shigowa gida domin ya san ba zai dawo ya tarar da bacin rai ba.


Wata kuma tace, muna zaune kawai sai yace min zai je su ci abinci da abokan shi domin an gayyace su wajen cin abinci. Ko kina bukatar wani abu kafin in fita? Da yake ita mai wayo ce kuma ta san abokai idan an hadu sai Allah, sai randa ta gan shi, kuma bata so tace mai kar ya dade kai tsaye. 


Sai tayi karaf tace masa eh dan Allah kar ka dade domin za'a dauke wuta. Sai yayi saurin juyowa gareta cikin mamaki yace mata wa ya fada miki wuta za a dauke? Tace ni na fada maka fitan ka kawai na sa gidan ko ina duhu ya rufe shi, amma da ka shigo sai ko ina ya haskaka komai yayi haske. Sai kawai yayi murmushi ya gane sakon da take bashi,  ya tafi cike da shaukin dawowa gida ba tare da ya tsaya dogon fira da abokanan shi ba.


Ita ko wannan cewa tayi, lokacin da miji na ya gama shiri zai fita sai nace ya bude bakin shi ya rufe idon shi, sai ya rufe idon shi ya bude baki yana jiran yaji mai za'ai masa, sai ta dakko cakulet da ta san yana so ta wurga mai a bakin shi. Bayan ya kai bakin kofa zai tafi sai ta sake ce mai haka. Yayi kasake yana jiran ya sake jin wannan cakuletin a bakin shi kawai sai yaji bakin ta cikin na shi ta sumbace shi ta ruga tana dariya tana daga mai hannu alamun bai-bai (Bye-Bye).


Shin a matsayinki na matar aure da kike yawan korafi akan mijinki, kina yi masa irin wadannan abubuwan? Idan kuwa har bakiyi masa irin wannan abubuwan to da sauranki. 


Fatan mata za'a Kula sosai a zamantakewar rayuwar aure, domin shi namiji kamar rakumi ne da akala. Yadda matarsa ta tafiyar dashi haka yake tafiya. 


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post