Akwai muhimman abubuwan da ake so Musulmi kwace mace-macen ta rika yi a duk lokacin da ta kammala yin Jima'i da mijinta.
Domin kula da lafiyar gabanki hadi da yadda za ki kasance kuma ki dauwamana da ni'ima na gamsar da mijinki a duk lokutan yin Jima'in ku. To ki kasance duk jima'in da za ki yi da shi kuma gamawa kiyi wadannan abubuwan kamar haka.
1: Abu na farko da zaki soma yi shine ki soma yin fitsari.
Yin fitsari bayan kammala jima'i yakan taimakawa mace kariya da fitar da duk wasu kananan halittun da suka shigeta fitar dasu ta hanyar yin fitsarin.
Kuma idan kinje yin fitsarin kada ki sakoshi lokaci guda kamar an kunce kan famfamfo ba. Kina yi kina matsaiwa da haka har ki kammala har sai kinji mararki babu saurin fitsarin sannan za ki mike.
2: Ki tabbatar kinyi tsarki ne da ruwa mai dumi ba mai sanyi ba.
Ruwan dumi yakan taimakawa mace gabanta ya koma yadda yake kamin yin Jima'in ta na lokacin. Haka nan ruwan dumin shima yakan halaka duk wasu cutukan da suka nemi shinga gabanta.
Tsarki da ruwan zafi bayan kammala Jima'i na mace na magance fitar iskan gaban mace, hakan yasa yake da kyau mata su kula.
3: Ki tabbatar kin wanke hannuwanki da kyau kamin ki baro bayan dakin (toilet) naku bayan gudanar da abubuwan da muka ambata a sama.
Yin hakan na kashe duk wasu cutukan da aka dauka ko za'a a dauka cikin yatsu ko hannu.
A lokacin jimai ko wasannin motsa sha'awa ma'aurata na amfani da hannu ko yatsunsu wajen yiwa juna wasa. A irin hakan ana iya samun cewa kwayar cuta ta makale ta hakan sai a sake fitowa da ita maimakon halakata a lokacin da aka shiga tsaftace jiki.
Don haka ki tabbatar kin tsaftace hannuwanki da yatsunki tsaf kamin ki fito.
4: Abu na hudu shine ki tabbatar da cewa kin sha ruwa mai yawa bayan yin Jima'in ki.
Wannan shan ruwan da duk mace zata yi bayan jima'i yakan maida mata da ruwan jikinta da ta rasa a lokacin wannan gumurzun da ake iya jika da gumi ko zufa.
Haka nan gaban mace idan mai saurin bushewa ne ruwan zai sake dawo mata da ni'imaarta. Baya ga hakan idan za ta gudanar da fitsarinta na biyu bayan Jima'i za ta karasa fitsari duk wata cutar da ta rage a mararta da bata fitar a fitsarin farko ba. Wannan yasa shan ruwan yake da amfani.
5: Kuskure ne mace ta sake maida kaya masu nauyi, ko jikanku cikinta musamman ma fant dinta. Ta nemi wasu kayan da basu da nauyi ta saka idan ba za ta iya kwanciya babu wando a jikinta ba.
Gaban mace yana bukatan samun iska bayan kammala Jima'i da kuma yi masa hidiman da muka ambata a baya.
Don haka sake matsai gabanta ko saka kayan da bazasu samarwa gabanta iska ba suna jerin abubuwan dake jawo gaban mace ya rika wari.
Da fatan mata ma'aurata za su kula da wadannan abubuwan domin samar da lafiyan gabansu.