Akwai matan da suke korafin cewa ba su da sha'awa, kuma basa damuwa Idan mazajensu ba su kusance su da niyyar yin Jima'i ba domin ko anyi Jima'i basa jindadi saboda babu sha'awa a tare dasu.
Sai dai akwai wasu abubuwan da ke jawowa matan rashin sha'awa wanda za mu bayyana muku su kamar haka :
1- Matsalolin Mara Da Mahaifa.
Kama daga sanyin mara (vaginities/toilet infections, UTI & STDs), yoyon fitsari, 'kululun mahaifa (fibroid), da sauran cututtukan al'aura, na daga cikin abubuwan da ka iya hana mace jin dadin jima'i.
Misali, sanyin gaba mai zuwa da 'yan 'kananan kuraje a cikin farji, na sanya mace taji zafi wajen jima'i, wanda sau da yawa masu kurajen basu ma san suna da kurajen a cikin al'aura ba, sai dai su ce su na jin zafi lokacin saduwa. Kurajen suna fashewa saboda gugar da ake yi musu yayin saduwa, sai wurin ya zama rauni.
2- Budewar Farji
Budadden gaba ga mace na sanya raguwar jindadi tsakanin ma'aurata. Sau da yawa ma'auratan biyu ba zasu samu gamsuwa ba da kyau, sannan macen baza ta iya jin 'kololuwar dadi ba shi ma namijin haka saboda rashin haduwar fata da fata yadda ya kamata.
3- Kaciyar Mata
Idan aka samu matsala wajen yiwa mace kaciya, ya zamanto an yanke beli da yawa fiye da yanda ya dace. Yin hakan na kashe sha'awar mace idan ta girma. Yanke beli da yawa ko duka matsalace dake hana mace jin dadin jima'i, domin kuwa beli shi ne matattarar jin dadin jima'in mace.
4- Magunguna
Yin amfani da magunguna ba bisa ka'ida ba. Yawaita shan magunguna barkatai kan iya ragewa mace sha'awa ko kuma ya sa ta dauke baki daya. Wani lokacin kuma ko da bisa ka'ida aka sha maganin to zai iya yiwuwa daga cikin side effect dinsa shi ne yana dauke sha'awa zuwa wani lokaci.
6- Rashin Abinci Mai Gina Jiki
Abinci mai gina jiki na nufin abincin da ke dauke da sinadaran da jikin mutum ke bukatarsu, to shi ne mai gina jiki a wajensa. Idan mace ba ta samun ingantaccen abinci za ta iya samun matsalar rashin sha'awa sosai.
7- Rashin Fahimtar Yanayin Mace
Wata matar ba wai sha'awar ce ba ta da ita ba, a'a. Ita kanta ba ta fahimci abinda zai sa mata sha'awar ba ne, shi ma mijinta bai fahimce ta ba, sai a tafi a haka, a matsayin ba ta sha'awa.
8- Wasa Da Gaba
Idan mace na wasa da farjinta (istimna'i) da yatsa ko wani abu da take sakawa, to zai dauke mata sha'awa kuma zai lalata ma ta gabanta da mahaifarta.
9- Matsalar Aljanu
Wata matar ana iya samun shaidanin Aljani ya shafeta, saboda ya ga yana sha'awarta. Sai ya dinga kishi da mijinta, don haka sai ya saka mata rashin sha'awa, sai dai in shi ya zo yana saduwa da ita a mafarki ta dinga jin dadi.
Rigakafin Rashin Sha'awa Ga Mata
Matar da ke gudun ta kamu da fadawa matsalar rashin sha'awa, ga wadannan shawarwari da za su amfane ku kamar haka.
1- Cin Abinci Mai Kyau
Idan da hali, yana da kyau mace ta dinga cin abubuwa masu gina jiki kamar Yoghourt, Hanta, Kwai, Zuma, Dabino, Aya, Gyada, Kankana, Ayaba da sauran abinci mai gina jiki. Duk matar da ke cin irin wadannan abubuwa to kullum cikin nishadi da sha'awa ta ke.
2- Fahimtar Yanayin Jiki.
Kowace mace tana da sha'awa amma kowacce da akwai wajen da anan ne sha'awarta ta fi karfi. Wata sha'awarta a tafin hannunta take, wata a kirjinta, wata a mazaunanta, wata a cinyoyinta, wata a lebenta, wata a wuyanta, da dai sauran sassan jiki. Ya kamata mace ta yi kokari ta gane babban wajen da idan mijinta ya taba ma ta take jin dadi, to sai ta yi masa bayani.
3- Aika Dan Aike
Yin wasanni kafin kwanciyar aure yana da matukar muhimmanci, mata suna son kafin a sadu dasu a fara yi musu wasannin da zai motsa musu da sha'awar su.
Illolin Rashin Sha'awa Ga Mace
1-Yana iya kawo rashin jituwa tsakaninta da mininta. Domin za'a yi ta samun fada tsakani, shi namijin zai rika tunanin matarsa ba ta son yin Jima'i dashi amma ita kuma rashin ba ta da sha'awa ne ya kawo hakan.
2- Ba lallai ta samu cikakkiyar lafiya ta murmure irin yadda matan aure suke yi ba, matukar ba ta samun kwanciya saboda rashin sha'awa za ka samu ba ta da cikakkiyar lafiya. Shi Jima'i yana kara lafiyar masu yinsa.
Da fatan wadannan bayanan nawa za su amfanar daku, kuma da fatan duk macen da ta san tana da wannan matsalar ta rashin sha'awa za ta dauki mataki ta hanyar da mukai bayani.
Allah yabamu lafiya da zaman lafiya