Abubuwan da ke jawo muku gajiya a jiki da yadda za ku magance su - Android Pols


Akwai abubuwa da dama da suke iya jawo gajiya ga jiki, sai dai wasu mutane da dama ba su san abubuwan da suke aikatawa ba dake iya jawo musu gajiya ga jikinsu ba. 


Hakan yasa muka tattaro muku wasu abubuwa da suke jawo gajiya ga jiki da kuma hanyoyin da za mu magance su kamar haka :


1. Rashin samun wadataccen barci;

Wani lokaci mutum yana samun kansa a yanayin da ba ya samun yin barci sosai. Wannan matsala ce da za ta iya shafar natsuwa da lafiyarka. Ya kamata mutumin da yake shekarun magidanci ya zamanto yana samun barci na tsawon sa'a bakwai zuwa takwas a duk dare. 


Yadda za ka magance matsalar: 

Ka ba wa barci muhimmanci kuma ya kasance ka tsayar da wani lokaci na barcinka a kullum.


Ka daina zuwa gado ko wurin barcinka da kwamfutarka ko wayarka kuma kar ka sa talabijin a dakin kwananka.


Idan ka yi duka wadannan amma kuma har yanzu kana samun matsalar rashin barcin, to sai ka yi kokari ka ga likita.


Zai iya kasancewa kana da larurar rashin barci ne.


2. Daukewar numfashi da munshari;

Wasu na ganin suna samun isasshen barci to amma a lokacin da suke tsakar barci sai numfashinsu ya rika katsewa kuma suna munshari, a dalilin haka sai barcinsa ya rika katsewa amma kuma ba tare da ya sani ba.


Duk da cewa ka shafe sa'a takwas a kan gado da sunan kana barci, to fa barcin da ya kamata ka samu bai samu ba. Likitanka zai iya gudanar da bincike a kanka game da wannan matsala.


Yadda za ka magance matsalar : 

Ka rage teba idan kana da teba. Ka daina shan taba idan kana sha. Kuma za ka iya samun na'ura ta musamman (CPAP) wadda take taimakawa mutum ya rika numfashi ba gargada a lokacin da yake barci.


3. Rashin cin wadataccen abinci;

Cin abinci dan kadan na sa mutum ya ji gajiya, kamar yadda cin abincin da bai dace ba ke zama matsala ga mutum.


Cin abincin da yake kunshe da abubuwan gina jiki yadda ya kamata na sa yawan sukarin jikinka ya zama daidai, kuma ya kare ka daga jin irin kasalar nan da idan sukarin ya yi kasa za ka ji.


Yadda za ka magance matsalsar: 

A ko da yaushe ka tabbatar ka karya kumallo, kuma ka tabbatar abincin ya kunshi sinadari mai gina jiki (furotin) da sauran sinadaran abinci da jiki ke bukata.


Misali, ka ci kwai da burodin alkama. Kuma ka tabbatar kana cin abinci kadan-kadan akai-akai domin ka kasance da kuzari a ko da yaushe.


4. Rashin isasshen jini ;

Rashin wadataccen jini na daya daga cikin manyan abubuwan da ke janyo wa mata gajiya.


Zubar jinin haila na iya sa mace ta rasa sinadarin da ke cikin jini mai muhimmanci da ke sa kuzari (iron).


Mutum na bukatar jini wanda shi ne ke daukar iska ya kai ta ga jijiyoyi da sauran sassan jikin mutum.


Yadda za a magance matsalar: 

Idan mutum yana da matsalar rashin wadataccen jini, wadda ta samu a dalilin karancin sinadarin cikin jini (iron). to yana bukatar ya rika cin abincin da ke dauke da wannan sinadari da kuma kwayoyin magani masu bayar da wannan sinadari.


Kayan abincin ya hada da nama da koda da kayan ruwa masu koko, kamar kaguwa da makamantansu da wake da dangin hatsi kamar alkama da makamantansu.


5. Ciwon damuwa;

Za ka iya daukar damuwa a matsayin wata larura ta tunani to amma tana haifar da wasu larurori na jiki da dama.


Gajiya da ciwon kai da rashin sha'awar cin abinci, wadannan suna daga cikin matsalolin da damuwa ke haifarwa.


Idan kana jin gajiya da kuma kasala sama da 'yan makwanni to kana bukatar ka ga likita.


Hanyar magancewa:

Ana samun sauki daga cutar damuwa ta hanyar tattaunawa da kwararru da kuma shan magani.


6. Karancin aikin sinadarin wuya;

Akwai wata 'yar karamar tsoka mai kama da kwaron nan malam-buda-mana-littafi a kasan wuyan mutum. Wannan halitta ita ke sarrafa yadda sinadaran cikin abincin da mutum ya ci ke zama karfi da mutum yake bukata ya yi aiki ko ya ji kazar-kazar.


Idan tsokar ba ta aiki yadda ya kamata, za ka rika jin kasala kuma za ka yi kiba.


Yadda ake magance matsalar :

Idan aka yi wa mutum gwajin jini aka gano cewa wannan tsoka ba ta aiki sosai, to za a iya sanya wa mutum ta roba wadda za ta taimaka wajen aikin ta ainahin.


7. Yawan shan sinadarin kofi;

Sinadarin kofi (Caffeine) ka iya kara wa mutum kuzari da natsuwa idan bai yi yawa ba.


To amma idan har mutum ya sha shi da yawa to zai iya karawa mutum bugun zuciya da bugun jini sanna kuma ya sa mutum karkarwa.


Wani bincike ya nuna cewa idan har mutum ya sha shi da yawa yana ma iya sanya wasu gajiya da kasala.


Yadda ake magance matsalar: 

A rage shan gahawa da shayi da cakuleti da lemon roba ko na kwalba ko na gwangwani da duk wani magani da yake dauke da sinadarin kofi.


Kada a daina sha lokaci daya domin hakan zai iya haifar da wata matsala da kuma karin kasala, sai dai a yi a hankali har a kai ga dainawa.


8. Cutar mafitsara;

Idan har ka taba kamuwa da cutar mafitsara (UTI), watakila ka san yadda mutum ke jin zafin fitsari da kuma yadda yake jin fitsari ya matse shi, ya nemi zuwa ya yi.


To amma kuma ba a ko da yaushe ba ne cutar ke zuwa da irin wadannan alamu na bayyane.


A wani lokacin mutum zai rika jin gajiya ne kawai, kuma idan aka yi wa mutum gwajin fitsari daga nan za a iya gano cewa yana dauke da wannan cuta ta mafitsara.


Yadda ake maganinta:

Ana bai wa mutum kwayoyin magani ne da ke iya kawar masa da ita, kuma ya daina jin gajiyar galibi cikin mako daya.


Yawan sukari kan tsaya a cikin jinin mutumin da ke da cutar sukari, maimakon sukarin ya bi jikinsa inda jikin zai sauya shi ya zama karfi ko kuzari.


Sakamakon wannan shi ne jiki zai kasance ba shi da kuzari duk da cewa yana da isasshen abincin da zai ci.


Idan kana yawan jin kasala maras dalili, to ka yi wa likitanka magana a yi maka gwajin cutar sukari.


Yadda za a yi maganin wannan: 

Maganin cutar sukari ka iya hadawa sauya yanayin abubuwan da mutum yake yi na rayuwarsa, kamar irin abincin da yake ci da motsa jiki da yin allurar sinadarin insulin da shan magunguna da za su taimaka wa jikin sarrafa sukarin da ke jikinsa.


9. Rashin ruwa a jiki;

Idan kana jin kasala watakila wannan alama ce ta rashin wadataccen ruwa a jikin ka. Ko kana aiki ne na waje ko kuma zaune a ofis kana bukatar ka rika shan ruwa domin ya sanyaya jikinka.


Idan har ta kai kana jin kishirwa to fa yanayi ya kai cewa babu ruwa a jikinka.


Yadda ake magance matsalar :

Ka rika shan ruwa duk tsawon rana ta yadda fitsarinka zai kasance ya yi haske.


Ka sha akalla kofi biyu na ruwa kafin ka kama wani aiki na motsa jiki.


Sannan kuma ka rika kurbar ruwan a yayin da kake aikin, kuma bayan ka gama ka sha akalla kofi biyu.


10. Cutar zuciya;

Idan ya kasance kana jin gajiya a lokacin da kake ayyukan da ka saba yi yau da kullum, kamar shara da goge-gogen gida ko gyaran lambu, to wannan ka iya zama wata alama ta cewa zuciyarka ba ta aiki yadda ya kamata ta yi.


Idan har ka ga cewa kana shan wuya ko gajiya a aikin da ka saba yi kafin ka gama, to ka hanzarta magana da likitanka kan ciwon zuciya.


Yadda ake maganin matsalar : 

Sauya yanayin rayuwa wato abubuwan da mutum yake yi da shan magani da matakai daban-daban na magani, duka wadannan ka iya magance matsalar cutar zuciya kuma su dawowa da mutum karfinsa.


11. Matsalar barci ta masu aikin dare ko karba-karba. 

Aikin dare ko kuma na karba-karba ka iya rikita yanayin aiki da hutun da jikinka ya saba da yi.


Za ka iya jin ka gaji a lokacin da ya kamata a ce kana farke. Kuma za ka iya kasa barci da rana.

Yadda za ka magance matsalar :


Ka rage zirga-zirga ko fitarka da rana a lokacin ya kamata ka huta.


Ka rufe dakinka ka kashe wuta ya yi duhu, ya zama shiru kuma ya yi sanyi.


Idan kana yin haka kuma ya kasance har yanzu kana samun matsalar rashin barci, to ka yi wa likitanka magana.


Magunguna da kwayoyi masu sinadarai ka iya taimakawa.


12. Cin abincin da jikinka ba ya so;

Wasu likitocin sun yi amanna cewa cin abincin da jikinka ba ya so ka iya sa ka jin barci.


Idan har ka cika jin kasala bayan ka ci abinci, zai iya kasancewa kana cin wani abinci ne da jikinka ba ya so - sai dai bai kai yadda zai sa jikinka kaikayi ba, illa kawai ya sa ka ji gajiya.


Yadda za ka magance matsalar : 

Yi kokarin barin wani abincin daya bayan daya ka ga ko matsalar za ta yi sauki.


Za ka iya neman likitanka ya yi ma gwajin kan-jiki na abinci, domin sanin irin abincin da ke sanya maka wannan matsalar.


13. Tsananin gajiya da kagewar jiki;

Idan gajiyar da kake ji ta wuce wata shida kuma ta yi tsananin da ba za ka iya jurewa ba, har ka rika yin ayyukan da ka saba na yau da kullum, to wannan na nufin kana da larurar tsananin gajiya ko kagewar jiki.


Dukkanin wadannan matsaloli ka iya nuna alamomi daban-daban amma babba daga cikinsu ita ce yawan jin kasala ba dalili.


Yadda za a magance matsalar : 

kasancewar babu wata hanya ta magance wadannan matsaloli biyu cikin sauri, mutum zai iya samun sauki ta hanyar sauya yanayin aikinsa na yau da kullum, misali ya sauya yanayin baccinsa ya kuma fara motsa jiki mai sauki.


Hanyar magance gajiya maras tsanani:

Idan kana jin kasala ko gajiya da ba ta da alaka da wani rashin lafiya, maganinta kila ba zai wuce motsa jiki ba.


Bincike ya nuna cewa manyan mutane da suke da lafiya, amma sukan ji gajiya ko kasala za su iya samun kuzari sosai ta hanyar motsa jiki.


A wani bincike, mutane na tuka keke wanda yake tsaye wuri daya tsawon minti 20 a hankali- a hankali.


Yin wannan sau uku a mako ya isa ya raba mutum da wannan matsala ta gajiya.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post