Abubuwa 6 Da Duk Macen Da Ke Yiwa Maisonta Su Mutuwa Kadai Ke Iya Rabasu - Android Pols



Gaba daya ita mace halayenta da dabi’un ta ke sa ta samu mijin aure sabanin namiji da ake iya hakura da wasu munanan halayen nasa mace ta aureshi.


Mafi yawan maza suna son su samu mace mai halaye da dabi'u masu kyau, shiyasa ko a cikin unguwa Idan akwai yarinya mai irin wadannan halayen za ka samu samari na rububin aurenta. 


Ga wasu halayen da maza basu cika bari mace mai irinsuba ba tare da sun aureta ba.

 

1: Mace Mai Yaba Kyauta: Namiji yakan yi saurin kamuwa da soyayyar macen daya fahimci ba ta raina duk kankantar kyautar da aka yi mata. Irin Wadannan matan nan take mazan da suke soyayya dasu suke burin ganin sun auresu.


2: Nuna Maka Soyayya Na Gaskiya: Ba duk maza ke sa'ar samun matan dake sonsu tsakani da Allah ba, yawancin soyayyar da mace za ta yiwa namiji da akwai wani abu a  dake haddasa hakan. Amma da zaran namiji mai hankali ya fahimci mace na masa so tsakaninta da Allah. Bai da wani burin da ya rage masa illa yaga ya mallaki wannan macen ta zama matarsa.


3: Mace Mai Tsaron Allah: Mata da yawa tsoron Allah su a baki ne bai cika kasancewa a aikace ba. Wannan yasa da zaran namiji ya ci karo da macen da take da tsoron Allah a cikin lamuranta na zahiri da badini. Allah-Allah yake yaga ya auri wannan macen kamin ta kubuce masa.

 

4: Mace Mai Iya Sadaukar Da Kai: Mazan da suka yi dacen gamuwa da macen da takan iya yi ko barin wani abu saboda soyayyar da take musu. Wannan macen bata kubucemusu basu aureta ba.


Ba duk mace bace za ta iya yi ko barin yin wani abunda ta saba yi ko take son yi saboda namijin da bata aureshi ba. Wannan yasa maza masu natsuwa Idan sun ci karo da irin wadannan matan, tabbatar wa suke sun zama matansu kamin suke samun natsuwa.


5: Macen Da Batada Boye Boye: Yana da wuya ka samu macen da za ta iya fitowa fili ta fadamaka gaskiyar yadda abu yake. Hakan yasa maza da dama basu cika yarda da daukan zantukan matan da suke aure ba bare ma na wacce basu aura ba.


Sai dai su maza masu natsuwa da zaran sun ci karo da macen da ba ta da nuku-nuku ko boye-boye, anan suke tabbatar da cewa sun ga matar aure.


6: Macen Da Ba ta Riko: Da yake shi lamarin aure lamari ne na yau da kullum. Hakan yasa maza suke gudun duk macen da ta cika mita ko dawo da abun da ya riga ya wuce a lokacin da aka samu wata matsala. Hakan kuma yasa da zaran namijin da ya san abunda yake yi ya ci karo da macen da take mantawa da abunda akayi ya wuce. A lokacin ne suke nuna sha'awar su na son aurenta.


Waɗannan suna cikin jerin abubuwan da maza masu hankali da natsuwa suke auna macen da suke burin ganin sun aureta tana da su ko ta gaza ta wadannan fanni.


Da fatan mata za a daure a siffantu da halaye da dabi'u masu kyau da za su iya jawo ribibin manema ba masoya ba.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post