Siyasa
Yanzu-Yanzu: Dan takarar jam'iyar PDP Kefa ya lashe zaɓen gwamna a jihar Taraba
Tuesday, March 21, 2023
0
An bayyana dan takarar gwamna na jam’iyyar PDP a jihar Taraba, Laftanar Kanar Agbu Kefas (mai ritaya) a matsayin wanda ya lashe zaben.
Kefas ya samu kuri’u dubu 236,712 inda ya doke ‘yan takarar New Nigeria Peoples Party (NNPP) da All Progressives Congress (APC), inda ya biyo baya a na uku.
Da ya ke yiwa manema labarai jawabi jim kadan bayan sanarwar, Kefas ya yi kira ga abokan takararsa da su hada kai da shi domin ciyar da jihar gaba.
A cewarsa, wannan nasara da aka samu wata manuniya ce ta yadda gwamnatin PDP mai ci a yanzu ta ke aiwatar da ayyukan ci gaba a jihar tun 1999.
Previous article
Next article
Leave Comments
Post a Comment