Yadda Aka Yi Amfani Da Giya Wajen Siyan Kuri'u A Jihar Benue - Android Pols - Android Pols - latest news, natural remedies, and entertainment

Yadda Aka Yi Amfani Da Giya Wajen Siyan Kuri'u A Jihar Benue - Android Pols


Ƙungiyar rajin kawo ci gaba ta YIAGA, ta ce bayanan da ta tattara sun nuna yadda Æ´an siyasa suka rinÆ™a amfani da abubuwa daban-daban wajen sayen Æ™uri’a a zaÉ“en gwamnonin Najeriya.


Jami’in Æ™ungiyar, Paul James, ya ce sun samu rahotannin sayen Æ™uri’u a jihohi da dama, ciki har da irin su Bauchi da Benue.


Ya ce a Makurdi, babban birnin jihar Benue, an rinÆ™a saya wa mutane barasa domin su kaÉ—a ma wasu 'yan takara Æ™uri’a.


Haka nan a cewarsa an yi amfani da kuɗi sosai a lokacin zaɓen na gwamnoni wanda ya gudana a ranar Asabar.


A tattaunawar da ya yi da BBC a safiyar Lahadi, James ya ce babban abin takaicin shi ne yadda wakilan jam’iyyu suka rinÆ™a kaÉ—a wa mutane Æ™uri’a bayan sun biya su kuÉ—i.


Ya kuma Æ™ara da cewa sun samu rahotannin wasu wuraren da aka Æ™ona Æ™uri’u bayan kai farmaki a rumfunan zaÉ“e.


Wannan zaben dai ya sha bamban da zaben da aka yi na shugaban kasa a makonnin da suka gabata inda a wannan zaben na gwamnoni aka samu yawan siyan Kuri'u duk kuwa da kiraye-kirayen da mahukunta suke yi akan hakan. 

Related Posts:
Previous article
Next article

Leave Comments

Post a Comment

Iklan Atas Artikel

Iklan Tengah Artikel 1

Iklan Tengah Artikel 2

Iklan Bawah Artikel