Za ka yi mamaki idan kaga mace ta makalewa namiji kuma a zahiri da badini tasan ba aurenta zai yi ba. Irin wadannan mazan da matan suke makalewa sun hada da:
1: Dan Hajiya: Shi Dan Hajiya sune irin yaran nan da iyayensu ke batasu da abun duniya.
Abunda zai baka mamaki zakaga mace tasan wannan bai da wani abun kansa sai yadda akayi da shi a gida. Amma mace ta nace wai shi take jira ya aureta.
2: Maza Masu Duka: Suma maza ne da mata suke nanewa. Namiji ne zai kama 'yar mutane da duka da suna soyayya, amma gobe tana gidansa tana gudun mazan dake lanlabanta su aureta.
3: Maza Masu Shaye Shaye: Zakaga budurwa ta makalewa bugagge da sunan zata aureshi.
Wani lokacin ma itake samo masa kudin da zai sayi kayan mayen. Amma ga wasu can ko goro basa ci suna nemanta da aure tana gudunsu.
4: Maza Masu Zaman Banza: Macece zata ce maka tana son aure, idan ka tambayeta wanda take so ta aura sai ta nuna maka wani can da bai da abunyi.
Abun haushi zakaga ga mazan da suka riga suka tara suna sonta amma ina, ita wannan dai da baida aikin komai take so.
5: Maza Masu Mugun Neman Mata: Su dai irin wadannan mazan bama sa zuwa gidan budurwa hira sai da ita ta zo. Abun takaici tana iya zuwa ta samu wata tare da shi, ko kuma yana kiran wata a waya. Amma ko a jikinta wai shi take so ya aureta.
Ka kula, akasarin matan da suke kokawa maza sun yaudaresu irin wadannan mazan ne da suka kai kansu kuma suka nace sai sun auresu bayan sunsan tun farko ba aurensu za suyi ba.
Mata abunda ya kamata ku fahimta game da aure shi, ba tsananin soyayya da kike yiwa namiji bane zai sa ya aureki ba. Haka kuma shi zaman aure ba dole sai wanda kike so zaki aura ba. Ki kula da wanda zai kiyaye hakkokin aurenki muddin akwai soyayya ko da kadan da kike masa gaba Zaki fahimci alherin zaben da kikayi.