Shin yin Istimna’i, kallon fina-finan rawa da tsiraici na karya azumi da yin kaffara? Tare da Imam Bello Mai-Iyali
TAMBAYA:Shin yin Istimna’i, kallon fina-finan rawa da tsiraici na karya azumi da yin kaffara?
AMSA: Alhamdu lillah, Tsira da Amincin Allah su tabbata ga shugabanmu Annabi Muhammad SAW.
Masturbation ‘IStimna’I’: shi ne Wasa da Al’aura, wanda a larabce aka sansa da “Istimna’i”. Wannan yana nufin yin amfani da hannu, yatsa ko wani abu domin biyan bukatar jima’i ga mutum da kansa da tunanin saduwa.
Hukuncin wannan (Istimna’i) da kallon tsiraici a musulunci Haramun ne kuma abin kyama ne. Hakika Haramcinsu na tsananta a cikin wata mai alfarma. Suna kekasar da zukata, kamar yadda suke rage Imanin bawa.
Wannan munanan dabi’u na masturbation (Istimna’i) da kallon tsiraici suna karya azumi matukar an zubar da maniyyi. Amma idan mutum bai fitar da maniyyi ba, to azuminsa nanan tare da cewa ya aikata mummunan laifin da Shari’ah ta Haramta.
Hukuncin mutumin da ya karya azuminsa da masturbation (Istimna’i) ko kallon tsiraici ko dukkanin wani abunda ya motsa sha’awa har aka zubar da maniyyi shi ne kamar haka:
1) Ya tuba zuwa ga Allah domin ya aikata harumun, kuma ya keta al-farman Ramadana.
2) Zai kame bakinsa duk da cewa azuminsa ya baci.
3) Zai rama azumin wannan rana (kadai) da ya bata.
4) Kuma zai gaggauta tuba da rama azumin.
5) Amma babu kaffara a kansa, domin ba jima’i ya yi ba.
Allah shi ne mafi sani. Allah ka tsaremana Imaninmu da mutuncin mu, Amin. Allah ka shiryar damu baki daya, Allah ya karbi dukkan ibadunmu da muke yi, Allah Kasa muna daga cikin yantattun bayin ka amin.