A rana irin ta yau 28 ga watan Maris na shekarar 2015 Ƴan Najeriya suka zaɓi Malam Muhammadu Buhari a matsayin Shugaban Ƙasa.
Miliyoyin yan Najeriya maza da mata samari da dattijai suka fito kwansu da kwarkwata suka Kada kuri'a domin neman canji. Wanda aka bayyana cewa shine zaben da mutane suka fi fitowa don kawo canji a tarihin kasar.
Zuwa yanzu dai shugaban kasa Muhammad Buhari ya shafe shekaru 8 yana mulkin Najeriya wanda yanzu dai saura kwanaki kaɗan ne suka ragewa Shugaban a mulkin da yayi na shekaru 8.
Da me zaku riƙa tunawa da shi?