Watan Azumin Ramadan wata ne mai cike da falala da Allah (SWT) ya ware shi da Musulmi suke yin azumi har tsawon kwanaki 29 zuwa 30.
Tambaya:
Assalamu Alaikum. Don Allah Malam a taimaka min da bayani game da dalilin da yasa ake yin Azumi?
Amsa:
Wa'alaikum assalam. Azumi ginshiki ne daga cikin turakun Musulunci, waɗanda addinin Musulunci ba zai cika ba sai da su. Allah da Manzonsa sun yi umarni da shi, saboda wasu muhimman manufofi, ga wasu daga ciki kamar haka:
1. Samun tsoron Allah, saboda mai Azumi yana barin abin da yake so saboda Allah, hakan zai sa ya ƙara samun tsoron Allah.
2. Samun kariya daga Shaiɗan, saboda Azumi yana takure hanyoyin Shaiɗan, wannan yasa zunubai suke ƙaranci a Ramadan.
3. Tuna talakawa da wahalar da suke ciki, saboda duk lokacin da mai kuɗi ya ɗanɗana yunwa zai tuna halin da talakawa suke ciki.
4. Sabawa rai wajen barin abin da take so, da kuma haƙuri akan abin da take sha'awa.
5. Kankare zunubai da kuma samun ɗaukakar daraja, saboda Azumi yana gyara zuciya, da kuma rai.
6. Samun lafiyar Jiki, saboda Azumi yana kariya daga cututtuka masu yawa, kamar yadda likitoci suka tabbatar.
7. Ta hanyar Azumi mutum zai saba da yin aiki don Allah, saboda AZumi sirri ne tsakanin Allah da bawansa.
Da fatan wannan fadakarwa za ta amfanar damu, kuma da fatan za mu yi aiki da abinda muka Karanta. Muna fatan Allah ya karbi ibadunmu amin.