Gwamnan Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya yi kira ga zaɓaɓɓen Gwamnan jihar Engr. Abba Kabir Yusuf da yayi haƙuri kar ya tsoma baki a al'amuran Gwamnati har sai an rantsar da shi.
A wata sanarwa da Kwamishinan Yaɗa Labaran Kano Malam Muhammad Garba ya fitar, ya yi martani kan shawarar da Abban ya bai wa masu gine-gine a filayen Gwamnati.
Ya ce, a kundin tsarin mulkin ƙasa har yanzu Dr. Ganduje ne Gwamna ba Abba ba, har zuwa ranar rantsuwa.
Saboda haka a yanzu duk abin da Gwamna yayi nasa ido ne, sai dai ya bari in an rantsar da shi sai yayi duk sauye-sauyen da zai yi.
Sanarwar ta ce, kuma fitar da filaye ai ba kanta farau ba, domin sanannen abu ne har a Gwamnatin da shi zaɓɓen Gwamna yayi aiki da ita a baya, wato dai Gwamnatin tsohon Gwamna Kwankwaso.
A ƙarshe sanarwar ta nemi waɗanda suka mallaki filayensu bisa ƙa'ida a ƙarƙashin Gwamnatin da su kwantar da hankalinsu.
Me zaku ce?