Sheikh Dr Sani Umar Rijiyar Lemo ya bayyana fatawowi akan shugabancin mace a musulunci.
1. An ɗora fatawar Dr. Sani a shafinsa na facebook 21st June, 2022.
2. Malamin ya yi bayani gamsasshe game da shugabancin mace a musulunci, inda ya naƙalto ijma'in malamai kan haramcin naɗa mace الولاية العامة, a matsayi kamar na shugaban kasa ko gwamna ko Alkali.
3. Malam ya kawo dalilai kan wannan ijma'i, tare da kawo zantuttukan waɗanda suke da saɓanin wannan ra'ayi da amsa garesu.
4. Bayan wannan shimfiɗar ne, malam ya yi bayanin hikimar shari'a a wannan matsayar inda ya ce mace ita take kulawa da gida kuma yanda Allah ya tsara halittarta, bata dace da wahalhalu na shugabanci ba, haka idan ta bar station ɗinta wanda shine gida, za'a samu matsala.
5. Sai malam ya yi magana kan tsarin shugabanci a dimokradiyya inda ya ce tsarin ya yi hannun riga da ƙa'idojin addinin musulunci ta yanda ya ba kowa daman tsayawa takara, babu bambancewa tsakanin namiji da mace.
6. Malam ya ce idan mace ta yi yunkurin tsayawa takara, ko da an mata wa'azi, ba dole bane ta saurara ta janye. Ya ce a wannan yanayi babu yanda ka iya da ita.
7. Sai malam ya kawo wata mas'ala, idan aka samu mace musulma ta tsaya takara, a gefe kuma arne ne, ya za'a yi kenan?
8. Sai malam ya ce الذكورية “mazantaka” sharaɗi ne babba a shugabanci, sai dai kuma a nan, yana iya zama cutarwa ga addinin musulunci, saboda duk da ba haka aka so ba, amma abune da ya fi sauki musulmai su zaɓi mace ƴar uwarsu da zasu iya mata magana dan kiyaye maslaharsu da su zaɓi wanda ba za su iya samun daman yi masa magana ba balle ya kiyaye musu mutuncinsu.
Ashe kenan, karo ne tsakanin sharuɗa 2 cikin sharuɗan da ake son mutumin da za'a zaɓa a matsayin shugaba ya cika su: addini da kasancewarsa namiji, wanne ne za'a gabatar idan ɗaya ne kaɗai za'a iya samu? Mahalli ne na ijtihadi cikin tsarin da ba na musulunci ba.
9. Wannan fatawar a fili take, babu ruɗu a ciki, kuma an bada amsa ne gwargwadon tambaya da aka yi tare da bada misalin yanayi da ka iya sa wasu musulmai saboda maslaharsu da halin lalura da suke ciki ka iya sa sauka daga asali.
Fatawar ba ta da alaƙa a zahiri da takarar wata, idan ma akwai sai dai mu alaƙanta ta da situation ɗin Kaduna inda mataimaki a jam'iyya ɗaya mace ne musulma, a ɗayan kuma namiji arne. Idan zaka yi i'itiradi, a nan ya kamata ka yi saboda shine daidai da misalin da malam ya bada.
10. Alaƙanta fatawar malam da situation ɗin Adamawa ba daidai bane saboda dalilai kamar haka:
-Ba a masa fatawa kai tsaye kan Adamawa ba, kuma situation ɗin Adamawa be dace da misalin da ya kawo ba.
-Cewa ƴan media sun sanya ma fatawar wani take suna amfani da ita wajen campaign ba dalili bane, saboda shima mai i'itiradi ana amfani da fatawar shi wajen tallata ɗan takaran PDP a Kaduna da hujjan cewa shugabancin mace haramun ne a musulunci.
-An yi primaries na ƴan tarakan gomnan Adamawa a APC May 26, 2022, wanda a lokacin babu wanda ya san duka yan takarkaru a duka jam'iyyu a jihar a lokacin. Duk da ma an soke zaɓen wace ta ci a APC lokacin kafin kotu ta maida mata daga baya.
11. Kaman yanda na yi ishara a tattaunawa ta da wani ɗan uwa Mal. Suhaib, lallai samun musulma gomna na iya zama fitina ga musulmai ta yanda za'a kafa hujja da wannan waqi'i wajen rusa asali, sai dai kuma idan aka ce lalura, dama abunda aka halatta a wannan yanayi ba halacci bane hukuncin shi a asali.
Kaman dimokradiyya ne karankanshi, asali haramun ne, kuma hatta a halin lalura ba kowa bane ya gamsu a shiga saboda lalura, wasu na ganin gwanda a mutu da a shiga, a yayin da me i'itiradi yake ganin a shiga saboda lalura ko da kuwa asalin hukuncin dimokradiyya a musulunci sananne ne, shine kuma kafirci.
12. Abun ban takaici ne ƙwarai malami ya ci mutuncin wani malami saboda yan media sun ingiza shi, ko da kuwa ba ruwan malamin da abunda ƴan media suka aikata. Haka abun takaici ne malami ya riƙa dogaro da gulma da ake kawo masa wajen hukunci.
13. Idan malami ya ce me yasa malam wane ba ze kawo fatawar malaman Saudiya ba. Yaushe fatawar malaman Saudiya ta zama shari'ah? Kuma wasu malaman? Na da ko na zamanin Ibn Salman? Saboda gwanda fatawowin malamanmu na gida yanzu da yawancin fatawowin da ke fitowa daga waje, Saudiya, Misra da sauransu.
Idan kuma na da malam ke nufi, toh ai mas'alolin da malam ya kawo shima be yi aiki da fatawarsu ba, saboda Bin Baz, Ibn Uthaimeen, Ibn Jibreen, Al-Fauzaan, duk basu dace da shi kan carbi ba, duk sun yarda za'a iya amfani da shi! Haka basu da qauli ɗaya kan hoto, wanda shi kuma ya maida shi mas'alar imani da kafirci, duk da tufka da warwara da ke cikin matsayin mai haramta hoto tare da halatta video (yayan hoto)!
©Ibrahim Usman Abu-Sultaan