A wannan takaitaccen rubutun za ku Karanta alamomin dake tattare da mace ko namiji idanun sun balaga. Da fatan za mu amfana.
Yin mafarki, kamar yadda aya ta: 59 a suratunnur ta tabbatar. Na daga cikin alamar farko da ake iya gane su mace ko namiji ya balaga.
Tsirowar gashin mara, da hamatta, sai an cika shekaru (15), kamar yadda Malamai suka bayyana haka a hadisin Ibnu-Umar lokacin da za’a fita Yakin Uhudu.
Fitowar nono, yana daya daga cikin alamu mafi saurin bayyana ga mace idan ta balaga, za'a ga nono ya tsiro ya fara girma.
Sai cenjin murya, musamman ga namiji yana daga cikin alamar balagarsa shine a ji muryarsa ta canja ta koma ta manya.
Sai qurajen fuska, wannan itama alama ce ta zahiri da ake iya saurin gane namiji ko mace sun balaga.
Duk alamar da ta fara zuwa ma da namiji ko mace daga cikin alamomi hudun da suka gabata, to ya zama baligi kuma shari’a ta hau kanshi matuqar yana da hankali.