Alamomin Da Ake Gane Mace Da Namiji Sun Balaga - Android Pols


Malamai sun raba yadda balagar namiji da ta mace take zuwa gida 4 da kuma yadda ake gane balagarsu. 


Ga jerin alamomin kamar haka ;


1 Mace idan tayi jinin al'ada koda tana yar shekara 9 da haihuwa, alama ce da ke nuna ta balaga. 


2 Namiji yayi mafarki maniyyi yafitar masa koda yana dan shekara 13, alama ce da ke nuna yaron ya balaga. 


3  fitowar gashi a mara, na daya daga cikin cikin alamu mafi saukin ganewa dake nuna mace ko namiji ya balaga. 


4 Ko da ba'a ga dukkan wadannan alamomin ba to idan sun kai shekaru 15 duk sun balaga.


Daga lokacin da 1 daga cikinsu ya cika wadannan abubuwan to girma ya kamashi, Kuma yasani cewa daga lokacin hukuncin shari'ar musulunci tafara aiki akansa.


Da yawan fatan iyaye za su saka idanunsu sosai akan yaransu domin gano halin da suke ciki da kuma hukuncin da ya rataya akan su idan sun balaga. 


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post