Celebrities
Kannywood
Labaran Kannywood
Yanzu-Yanzu: Kotu A Kano Ta Aike Da Murja Kunya Zuwa Gidan Yari
Thursday, February 2, 2023
0
Kotun shari'ar Muslunci da ke Filin Hoki a Kano ƙarƙashin mai Shari'a Abdullahi Halliru ta aike da Ƴar TikTok ɗin nan Murja Ibrahim Kunya zuwa gidan yari.
Lauya Barrister Lamiɗo Abba Soron Ɗinki ya karanto mata ƙunshin tuhume-tuhumen da ake mata wanda ta musanta.
Ana zargin Murja da É“ata suna da barazana ga Aisha Najamu ta Izzar So da kuma Ashiru Idris wanda dukanninsu abokananta ne.
Kotun ta ɗage sauraron ƙarar zuwa 16 ga watan Fabrairun da muke ciki.
Sai dai Lauyan Murja Barrister Yasir Musa ya nemi a tura ta zuwa Hisbah maimakon gidan Yari sai dai Kotun bata amince ba.
Previous article
Next article
Leave Comments
Post a Comment