Breaking News
Labaran Duniya
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bada Umarnin cigaba da amfani da tsohuwar Naira 200
Wednesday, February 15, 2023
0
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bai wa babban bankin ƙasar umurnin ya sake fito da tsofaffin takardun naira 200 domin a ci gaba da mu'amala da su a ƙasar.
Shugaban ya bayyana haka ne a cikin jawabin da ya yi wa al'ummar ƙasar da safiyar ranar Alhamis.
Buhari, wanda ya ce yana sane da irin halin wahala da al'ummar ƙasar ke ciki, ya ce za a ci gaba da amfani da takardar kuɗin ta naira 200 har zuwa 10 ga watan Afrilu.
Ya kuma buƙaci al'umma da su ƙara haƙuri kan halin da ake ciki.
Previous article
Next article
Leave Comments
Post a Comment