Shi dai harshen Turancin Ingilishi ya samo asali ne tun daga kasar Ingila da wasu kasashe dake yankin nahiyar Turai.
Harshen Turancin Ingilishi dai ya zama kamar abin ado a wasu gurare a nahiyar Afirka, inda wasu da basa jin yaren ake yi musu kallon ba su waye ba.
A nahiyar Afirka kasashe da yawa sun mayar da yaren Turanci a matsayin yare na daya wajen gudanar da harkokin yau da kullum har ya zama abin gasa inda wasu kasashen suke ganin sune suka fi iya harshen.
A Wannan video za ku ji wani rahoto akan wasu kasashe guda 6 a Africa da suka fi iya kwarewa wajen iya Turanci.