Wannan tsarin da akeso a tabbatar dashi a wannan ƙasar tamu na Cashless Policy zaizo da abubuwa da dama musamman Cyber Crime irinsu Fake Alert, kutsen asusun banki makamantansu.
Don haka dole mu koyi sanin yadda zamu gane waɗannan abubuwan domin kare kawunan mu daga faɗawa hannun macuta kuma yan damfara, tun kafin Nigeria tashiga wannan tsarin na Cashless andaɗe anayin Fake Alert kuma an daɗe ana cutar mutanen mu yan kasuwa da wannan tsarin musamman masu POS.
Shiyasa a wannan bidiyon muka kawo muku hanyoyin da za ku gane idan an turo muku kudi na gaskiya da na karya.