Yan Hisbah Sun Cafke Wani Kasurgumin Boka Kan Laifin Yiwa Wata Mata Ciki - Android Pols - Android Pols - latest news, natural remedies, and entertainment

Yan Hisbah Sun Cafke Wani Kasurgumin Boka Kan Laifin Yiwa Wata Mata Ciki - Android Pols



Hukumar Hisbah ta jihar Kano a arewacin Najeriya ta kama wani boka da ake zargi da yi wa wata mata ciki bayan ta je wajen sa neman magani.


Bokan mai suna Muhammad Mansur, mazaunin karamar hukumar Dawakin Kudu an kama shi bayan matar da ba a bayyana sunanta ba, ta kai kara tana neman a bi mata hakki dauke da cikin wata bakwai.


Rahotanni daga garin na nuna cewa bokan ya yi fice wajen yaudarar mata, ciki har da matan aure.


Bokan na yaudarar mata ta hanyar shaida masu cewa idan suka kwana da shi zai ba su maganin da zai hana a yi masu kishiya da kuma samun damar mallakar miji.


Ta faÉ—a wa Hisbah cewa lokacin da ta je neman maganin wajen bokan ya shaida mata cewa ba zai yiwu ba, sai sun kwana tare.


A cewar ta, mutumin ya jima yana neman saduwa da ita, idan sun je wajen tare da mahaifiyarta, amma bai yi nasara ba har sai lokacin da ta ziyarce shi ita kaÉ—ai.


Bokan, Muhammad Mansur ya amsa wannan laifi, sai dai ya ce aikin shaiÉ—an ne.


Shugaban rundunar Hisbah reshen karamar hukumar, Ustaz Kabiru Musa Dawakiji, ya ce za su ci gaba da bincike domin É—aukan mataki.

Related Posts:
Previous article
Next article

Leave Comments

Post a Comment

Iklan Atas Artikel

Iklan Tengah Artikel 1

Iklan Tengah Artikel 2

Iklan Bawah Artikel