'Yan Bindiga Sun Kashe Wani Ango Kwana Daya Kafin Daura Aurensa - Android Pols


Wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun kashe wani matashi mai suna Izuchukwu Charles Igweka, kwanaki biyu kafin  daurin aurensa a jihar Anambra. 


An tattaro cewa lamarin ya faru ne a garin Ukpor dake karamar hukumar Nnewi ta kudu da misalin karfe 10 na daren Laraba, 5 ga watan Janairu, 2023. 


Marigayi Izuchukwu an shirya za'a daura aurensu bisa al'ada tare da matarsa, Chinenye Linda Chukwuchekwa a ranar 7 ga Janairu, a Ezekwuabo-Otolo Nnewi. 


"Yana da wuya yin bankwana da dan uwa amma Allah ne mafi sani, Najeriya ta faru da kai kuma Najeriya ta gaza ka dan uwa," Obi  ya rubuta.   


Kamar jiya muke yin rayuwa tare yau kuma gashi babu shi, na yi fatan ci gaba da ganin abokina muna yin rayuwa tare domin akwai abubuwan da muke so mu yi a rayuwa, nayi bakin ciki da ban iya yin komai ba lokacin da yan bindiga suka kashe min aboki. 


Mun yi rayuwa mai yawa cikin aminci da inganci amma suka zabi su kashe ka suka rabani dakai, aurenka da muka dauki lokaci muna shiri da za'a daura a ranar 7 ga watan Janairu amma suka dauki rayuwarka don rashin imani. 


Babu abinda zan fadi game da kai abokina da ya wuce ban kwana mafi muni a wajena, ba zan taba mantawa da kai a matsayin aboki, amini kuma dan uwa ba. Ina matukar kaunarka har abada, cewar Obi.  

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post