Rundunar 'yan sandan jihar Kano ta yi nasarar kame matashin da ya kashe matar mahaifinsa da yarta 'yar shekara 8 da haihuwa.
Matashin da ake zargi da yin kisan mai suna Gaddafi Sagir dan shekaru 20 an yi nasarar kama shi a wani kango yayin da yake kokarin tserewa daga Kano.
Ko da ake tambayarsa matashin ya amsa laifinsa inda yace ya yi amfani da sukundireba ya dabawa matar babansa a wuyanta sannan kuma ya toshe bakin yarta har sai da ta daina yin numfashi.
Lamarin dai ya faru ne tun a ranar 07/01/2023 Sagir Yakubu mijin Rabiatu bayan ya dawo gida ya riske matarsa da yarta Munawwara yar shekara 8 kwance sun mutu cikin jini wanda yai zargin dansa Gaddafi da aikata hakan.