Wani fitaccen boka mai suna Fadayomi Kehinde da ake yi wa lakabi da (Ejiogbe) a garin Ikere-Ekiti a Jihar Ekiti ya mutu a ranar Litinin da ta gabata lokacin da yake lalata da matar wani Fasto a otel.
Ana zargin matar Faston tana dauke da wani tsafin Yarbawa da ake kira Magun (Tsawa) da mijinta ya yi ba tare da saninta ba.
Yarbawa sun camfa cewa Magun yana hallaka duk mutumin da ya yi lalata da matar aure nan take kamar yadda ya rutsa da Boka Ejiogbe.
Matar Faston da aka sakaya sunanta ta yi wa jami’an tsaro bayanin cewa jim kadan bayan bokan ya gama lalata da ita a cikin dakin sai ya fadi kasa yana shure-shure da neman ta taimaka masa ta gayyato masu kula da dakunan otel din domin ceton ransa.
A lokacin da aka kai bokan wani asibiti a garin na IkereEkiti, likitocin sun tabbatar da mutuwarsa tun kafin su fara yi masa aiki.
Mutuwar Boka Ejiogbe ta sa wasu fusatattun mabiyansa sun cocin da Faston kuma mijin matar yake shugabanci inda suka lalata wasu sassan ginin cocin.
Matar Faston tana tsare a hannun ’yan sanda suna yi mata tambayoyi tare da kare ta daga fadawa hannun fusatattun mabiya bokan.