Yadda Jaruma Rahama Sadau Take ci Gaba da Daukan Sabon Fim Dinta a Kasar India - Android


A yanzu haka jarumar fina-finan Hausa (Kannywood) da Kudancin Najeriya (Nollywood) Rahama Sadau na ci gaba da daukan sabon fin din da su ke yi a kasar India.


Wannan fim dai su na daukan sa tare da Jarumin kasar India wato Rajneesh Duggal kuma an dauki lokaci ana gudanar dashi. 


Rahama Sadau dai ta kafa tarihin kasancewa jarumar da ta ke yin fina-finai a masana'antun shirya fina-finai guda uku (3) kenan wato Kannywood da Nollywood da kuma Bollywood.


Jama'a dai da dama ne ke ta bayyana ra'ayoyinsu wasu na ganin cigaban jarumar ne yayin da kuma wasu ke yin tofin Ala tsine.


Shin ku menene ra'ayin ku akan wannan batun, kuna ganin cigaba ne ko akasin hakan? Ku bayyana mana ra'ayoyin ku. 

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post