An samu gawar wata mata ta mutu a cikin gidanta da ake zargin karnukanta sun cinye biyo bayan koke-koke da makotanta suke yi cewa wani mummunan wari na damunsu".
An kira 'yan sanda zuwa wata unguwa dake titin filin jirgin sama, a birnin Santa Rosa, Argentina, biyo bayan rahotanni daga makwabta game da wani "Wari" da ke fitowa daga gidan na tsawon mako guda.
Lokacin da suka shiga gidan, a ranar 31 ga Disamba, sun gano gawar matar Ana Inés de Marotte, wacce karnukanta guda biyar suka cinye.
A cewar shafin Infopico, an bayyana matar mai shekaru 67 a matsayin " ta bata" a cikin mako na biyu na Disamba, amma an same ta a Santa Rosa Sanatorium kuma aka sake ta a wannan rana.
Ta tafi Santa Rosa Sanatorium don jinyar rashin lafiya kuma an shigar da ita ba tare da dangi a cikin birni ba.
Bayan sallamarta, Marotte ta koma gidanta kuma an same ta bayan mako guda tare da karnukanta a makale a gidan tare da ita.