Yadda aka kame wani saurayi yana wanka da jini a cikin wani kwari



A ranar Alhamis din makon jiya ne ’yan sanda a Jihar Ogun suka kama wani mazaunin unguwar Obantoko da ke Abeokuta, babban birnin Jihar Ogun, bisa zarginsa da laifin yin wanka da jini a wani kogi.


Ana dai zargin mutumin mai suna Ganiyu Shina, mai shekara 49 da yi wankan a wani kogi da ke Unguwar Kotopo a karamar Hukumar Odeda da ke jihar.


Sanarwar da Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar, SP Abimbola Oyeyemi ya fitar, ta ce an kama wanda ake zargin ne a lokacin da jama’ar yankin suka gan shi a bakin kogi, ya ajiye motarsa kirar Nissan, ya fito da soso na gargajiya (kankan) da wata roba cike da jini ya fara wanka da shi.


“Da ya gano cewa mutane suna kallon sa, sai ya ruga a guje, amma jama’ar unguwar suka bi shi suka kama shi.


Shugaban al’ummar yankin ne ya ankarar da ’yan sandan da ke Aregbe, inda nan take DPO din yankin SP Bunmi Asogbon ya jagoranci ’yan sintiri zuwa wurin,” in ji Oyeyemi.


Ya ce da aka yi masa tambayoyi, wanda ake zargin ya yi ikirarin cewa yana da matsalar aljanu, kuma wani boka ne ya umarce shi ya yi wanka da jinin, inda ya ce jinin da ke hannunsa ba na mutum ba ne, na saniya ce.


Tuni Kwamishinan ’Yan sandan Jihar, Lanre Bankole, ya bayar da umarnin a dauki ragowar jinin domin bincike a dakin gwaje-gwaje, don gano ko na mutum ne ko a’a.


Kwamishinan ya yaba wa al’ummar yankin kan rashin daukar doka a hannunsu, kuma ya ba su tabbacin za a binciki wanda ake zargin yadda ya kamata.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post