A wata hira da gidan Freedom Radio yai da jarumin fina-finan Hausa Sadik Sani Sadik ya caccaki masu cewa ƴan film suna koyar da tarbiyya ne.
Sadik ya ce, tarbiyya tun daga gida ake yinta saboda haka shi ba tarbiyya ya zo koyarwa ba kuɗi yazo nema.
Jarumin ya kuma jaddada maganar da ya yi a watan da ya gabata ta cewa, yana fatan ya mutu yana film, yana mai cewa, ko kaɗan bai yi nadamar faɗin hakan ba.
Ga cikakkiyar hirar da aka yi da jarumin 👉Video