Habiba Hassan wacce fitacciyar mawakiya ce a masana'antar Kannywood ta yi Kira ga samari musamman wadanda ke zuwa neman aurenta da su daina wahalar da kansu.
Mawakiyar ta bayyana hakan ne a wata hira da ta yi da gidan Radio Freedom Kano inda ta ce bata bukatar yin soyayya da saurayi saboda irin yaudarar da suka yi mata a baya.
Ta Kara da cewa a duk lokacin da ta tuna irin yadda samari suka yaudareta a baya sai ta ji ba ta son kara kuka wani namiji saboda irin tsantsar yaudarar da akai mata.
Yanzu wanda zan aura nafi son samun namiji wanda ya taba yin aure ko yake da mata domin sun fi sanin darajar mace fiye da saurayin da bai yi aure ba, inji ta.