Fitaccen mawaki a Masana’antar Kannywood Ali Isah wanda ake yiwa lakabi da Ali Jita ya bayyana cewa nan ba da jimawa ba zai daina yin waka domin yan so ya zama daya daga cikin fitattun masu karatun Qur'ani a fadin duniya.
Ali jita ya bayyana hakan ne a shafinsa na instagram a ranar Laraba. Inda yace yana dab da ajiye sana'ar buga waka domin ya koma Karanta Al-qur'ani maigirma.
Yace burinsa shine ya kasance daya daga cikin fitattun mutane makaranta al-qur'ani maigirma a duniya.
Dubban mutane dai sun yi tsokaci akan kalaman mawakin inda suke ta yi masa fatan alheri da addu'ar Allah ya cika masa burinsa.