Mu 'Ya'yan Tinubu Da Ganduje Ne, Cewar Wasu Daga Cikin Jaruman Kannywood - Android Pols
Fitacciyar furodusa kuma jaruma, Mansurah Isah, ta bayyana cewa Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na Jihar Kano shi ne ya É—auki ‘yan fim na Kannywood ya miÆ™a su ga É—an takarar shugaban Æ™asa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, shi ya sa ake ganin kusan dukkansu su na tafiyar jam’iyyar ne.
Masu lura da harkokin masana’antar finafinan sun ga yadda ‘yan fim su ka yi dumu-dumu a cikin harkar siyasa a wannan lokacin, amma a maimakon yadda su ke raba Æ™afa a baya sai su ka bayar da Æ™arfin su a É“angare guda.
Kusan kowane jarumi ko mawaÆ™i da ya shahara da wuya ka ji ba ya tafiyar jam’iyyar APC, kuma wasu jaruman da a da ba sa shiga harkar siyasa sai a bayan fage, yanzu sun fito tare da su ake tafiya tallar Tinubu.
A ganin wasu masu lura da al’amuran Kannywood, bin É—an takara É—aya tilo kamar ragon azanci ne.
Da mujallar Fim ta tambayi Mansurah Isah nata dalilin na yin dumu-dumu cikin harkar siyasa tare da dunÆ™ulewar su ‘yan fim a waje guda, sai ta ce: “To da man ni ina siyasa ana ba ni aikin talla da kuma wasu ayyuka, amma dai ban taÉ“a shiga harkar na yi yawo ina bikin É—an takara ba sai a wannan lokacin.
“Kuma ba ni kaÉ—ai ba, mu na da yawa mata da Maza na cikin Kannywood.
“Amma dai a yanzu mun lura da halin da ake ciki, don haka mu ka fito mu nemi ‘yancin mu ta hanyar shiga siyasa da kuma zaÉ“ar É—an takarar da zai kawo mana cigaba da zaman lafiya a Æ™asar mu.”
A kan dalilin su na bin Tinubu, Mansurah ta ce, “A nan Kano kowa ya sani mu ‘yan fim ‘ya’yan Baba Ganduje ne kuma da yake É—an takarar shugaban Æ™asa na APC Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, mutum ne da ya ke son ‘yan fim, to da ya zo Kano sai Baba Ganduje ya ce, ‘Ga ‘ya’ya na, na ba ka su ka yi tafiya da su don za su yi amfani a yaÆ™in neman zaÉ“e.’ Kuma alhamdu lillah an É—auke mu a matsayin ‘ya’ya duk inda za a je ko a jirgi ko a mota da mu ake zuwa.
“Don haka duk wani dan fim a Kano É—an Baba Ganduje ne, don shi baban mu ne kuma masoyin mu ne. Tsakanin mu da shi sai godiya.”
Leave Comments
Post a Comment