Rundunar ‘yan sandan jihar Kwara ta kama wani matashi mai suna Issa Naigheti kan zarginsa da yin garkuwa da mahaifinsa tare da karbar kudin fansa N2.5m.
Kakakin rundunar ‘yan sandan Ajayi Okasanmi, ya ce jami’an rundunar da ke yaki da masu garkuwa da mutane na rundunar ‘yan sandan jihar Kwara ne suka kama wanda ake zargin a unguwar Kambi da ke Ilorin.
“Wanda ake zargin ya amsa laifin da ake tuhumarsa da hada baki da wasu mutane biyu domin yin garkuwa da mahaifinsa, Bature Naigboho a yankin Igboho/Igbeti a jihar Oyo tare da karban kudin fansa N2.5m.
”Okasanmi ya kuma kara da cewa za a mayar da shari’ar zuwa jihar Oyo, inda nan ne aka aikata laifin.
Lamarin dai ya tayar da hankalin al'umma sosai inda suke ta yin Ala wadai duba da irin yadda matashin ya nuna rashin imani ga mahaifinsa.
Za'a iya cewa wannan ba shine karon farko da wasu ke yin garkuwa da mahaifansu domin su karbi kudin fansa ba.