Wata malamar makaranta 'yar kimanin shekaru 42 da haihuwa ta bayyana yadda take matukar bukatar namijin aure.
Ta bayyana cewa ita malamar makaranta ce kuma ta shafe tsawon lokaci tana koyarwa amma haryanzu ba ta samu mijin aure ba.
Matar ta wallafa a shafinta na Twitter, inda ta sanar da mabiyanta masu amfani da kafafen intanet cewa ba ta yi aure.
"Ina da shekaru 42 ina neman wanda zai aureni domin ya zama uban 'ya'ya na. Ni Kwararriyar malama ce da na kware a koyarwa."
Yawancin masu amfani da Twitter sun mayar mata da martani ta hanyoyi daban-daban.