HOTUNA: Yau ko bakaso sai mun baka Sarautar Jarumin Karshi, Inji Sarkin Karshi ga Kwankwaso - Android Pols


Mai Martaba Sarkin Karshi Farfesa Sani Mohammad Karshi III, ya baiwa Engr Dr Rabiu Musa Kwankwaso Sarautar Jarumin Karshi, bisa irin namijin kokarin da yake yi wajen riko da gaskiya da Amana.


Farfesa Sani yayi jawabi tare da nuna Jin dadin sa da yadda Sanata Kwankwaso yayo tattaki da sanyin Safiya domin ziyartar masarautar.


A jawabinsa Engr Dr Rabiu Musa Kwankwaso yayi godiya da wannan kyauta da aka bashi tare da yin alkawarin ci gaba da kulla kyakkyawar alaka ga wannan masarauta.


A tare da tawagar sa akwai Mataimakin sa Bishop Isàac Idahosa, Engr Buba Galadima da Dan takarar Gwamnan Jihar Nassarawa a Jamiyyar NNPP da mataimakin sa da dai sauransu.







Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post