Gobarar ta tashi ne da misalin karfe 8 na daren ranar inda ta kone Shaguna masu tarin yawa tare da asarar dukiya mai girman gaske a kasuwar potiskum dake jihar yobe a arewacin Nigeria.
Inda aka yi asarar dukiya mai girman gaske, wutar ta tashi daga tsakanin kasuwar ƴan gwanjo, ƴan kekuna da masu doya
Hukumar kashe gobara ta isa wajen akan lokaci inda sukayi nasarar kashe wutar tare da taimakon jama'a.