HOTUNA: Yadda Aka Yi Janaizar Jarumin Kannywood Abdulwahab Awarwasa - Android Pols - Android Pols - latest news, natural remedies, and entertainment

HOTUNA: Yadda Aka Yi Janaizar Jarumin Kannywood Abdulwahab Awarwasa - Android Pols




Daya daga cikin fitattun jarumi a masana'antar Kannywood Abdulwahab wanda aka fi sani da Awarwasa ya rasu a yammacin ranar Litinin a garin Jos bayan fama da gajeriyar rashin lafiya.


Shi dai Awarwasa daya ne daga cikin manyan yaran jarumi Ali Nuhu, kuma Dan asalin unguwar Fagge ne dake cikin birnin Kano kuma yaki dade ana damawa dashi a masana'antar Kannywood inda ya ke fitowa a matsayin dan daba.


Baya ga fitowa da yake yi a finafinai, Awarwasa furodusa ne da ya shirya fina-finai da dama tun tsawon lokaci. Inda aka ce ya kwan biyu yana fama da rashin lafiya har daga baya ya koma garin Jos don neman magani inda a can Allah yai masa rasuwa.


Awarwasa yana mata daya da yara 3, tuni dai an yi Janaizarsa kamar yadda addinin musulunci ya tanadar.


Da yawa daga cikin abokan sana'arsa na Kannywood sun halarci Janaizarsa da aka yi a makabartar kofar mazugal dake birnin Kano.









Related Posts:
Previous article
Next article

Leave Comments

Post a Comment

Iklan Atas Artikel

Iklan Tengah Artikel 1

Iklan Tengah Artikel 2

Iklan Bawah Artikel