Jaruma a masana'antar Kannywood, Hajiya Maryam Sulaiman wacce aka fi sani da Maryam CTV, ta ce rashin fitowar ta a cikin fim a yanzu ba shi da alaƙa da ko ta daina yin fim, ta ce har yanzu ta na yi.
Jarumar, wadda ta ƙware wajen fitowa a matsayin matar attajiri har ake yi mata laƙabi da Hajiyar Falo, ta bayyana haka ne a lokacin da ta ke tattaunawa da mujallar Fim kan labarin da ake yaɗawa cewa wai ta daina yin fim. Maryam CTV ta ce:
“Ni ban daina yin fim ba. Har yanzu ina nan ina yi, amma dai ba kamar yadda aka san ni ina yi a baya ba. A yanzu ina yi ne kaɗan-kaɗan.”
Da ake tambayar ta dalilin hakan, sai ta ce, “To, da man can ni ‘yar siyasa ce. Ina cikin harkar siyasa, don haka a yanzu da aka koma harkar siyasa, sai ya zama na rage fitowa a fim saboda harkar siyasa da na ke yi a yanzu.
“Don haka mutane su daina ganin kamar na bar harkar fim. Ban bari ba. Ina yi, sai dai ba sosai ba.”
Hajiya Maryam ta miƙa saƙo ga masoyan ta, ta ce: “Ina yi wa dukkan masoya na fatan alheri da su ka damu da ni har su ke tambaya ta. Allah ya ƙara haɗa kan ‘yan fim, ya kawo mana cigaba a cikin masana’antar Kannywood baki ɗaya.”