Wata mata mai suna Ramlat Alh Shehu Aji an yi garkuwa da ita a hanyarta ta zuwa jihar Katsina daga Kagara a karamar hukumar Rafi a jihar Neja bayan ta bayyana inda ta ke a Facebook.
Ramlat a ranar Sabuwar Shekara, Janairu 1, 2023, ta wallafa a shafinta na Facebook cewa tana kan hanyarta ta zuwa Funtuwa amma bata isa inda zata nufa ba.
Kawar ta , Aisha Nasafe ta tabbatar da cewa wasu ‘yan bindiga da ake kyautata zaton ‘yan bindiga ne suka sace ta a Birnin Gwari, Kaduna.
Wani da ya wallafa labarin a shafinsa na Facebook Alhaji Abdullahi Dan Gaske ya bayyana cewa yanzu tilas ne mutane su Kula wajen wallafa labarin inda suke a kafafen sada zumunta.
Masu yin garkuwa da mutane sun yadu a ko ina a shafukan sada zumunta kuma suna ganin dukkan abubuwan da kowa yake yi, cewarsa.