Rundunar ‘yan sanda a jihar Legas ta cafke wata uwa da abokin zamanta bisa zargin yi wa ‘ya’yanta biyu masu shekaru 5 da 2 dukan tsiya.
Matar mai suna Busola Oyediran da mijinta, Akebiara Emmanuel, ‘yan sanda sun kama su ne a ranar Juma’a, 13 ga watan Janairu, biyo bayan rahotannin da makwabta suka samu.
Makwabtan da abin ya shafa sun sanar da ‘yan sanda game da cin zarafin kananan yara da mahaifiyarsu ta haifa da abokin zamanta suka yi.
Bayan wannan rahoto, ‘yan sanda sun mamaye gidan ma’auratan Egbeda/Idimu tare da kama su. Daga bisani ‘yan sandan sun ziyarci asibitin da makwabta suka kai yaran da aka yi wa duka domin yi musu magani.
Lokacin da ake yi mata tambaya kan dukan yaran, mahaifiyarsu ta ce yaran sun fado daga babur kuma sun sami munanan raunuka.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Benjamin, ya ce ma’auratan suna tsare a halin yanzu kuma za a gurfanar da su a gaban kotu a ranar Litinin ga watan Janairu. Ya ce an sanar da mahaifin yaran.