Wata amarya da ya rage kwanaki 12 a gudanar da bikinta ta rasa ranta a wani hatsarin mota da ya rutsa da ita.
Hon Aliyu Yalwa Tsafe shine ya wallafa labarin mutuwar budurwar a shafinsa na Facebook inda yai rubutu kamar haka.
"Innalillahi Wa'inna Ilaihin rajiun.😭😭
Innalillahi wa, inna ilaihin rajiun.😭😭
Innalillahi wa inna ilaihin rajiun.😭😭
Yau saura kwana 12 a daura masu aure amma Allah mai kowa mai komai ya yima amaryar rassuwa sanadiyar hatsarin mota Allah yajiqanta da rahama shikuma Aliyu Usman Fulani Allah ya bashi hakuri da juriya allah yaimata rahama."