Wasu zafafan hotuna da Fitacciyar jaruma Rahama Sadau ta wallafa a shafinta na Instagram na bikin zagayowar shekarar da aka haife ta sun jawo Cece-Kuce inda jama'a ke ta bayyana ra'ayoyinsu.
Wasu dai na yi mata murna day zagayowar ranar da aka haife ta wasu kuwa na bayyana ra'ayin su akan irin suturar da ta saka na ganin rashin dacewar yin hakan.