Masu magana na cewa komai lokaci ne, a yau dai jarumi Yusuf Muhammad Abdullahi wanda aka fi sani da Saseen ya zama ango tare da amaryarsa Amina Zakari Yunusa.
Shafin "Film Magazine" ya rawaito cewa daura auren ne da karfe 11:00 na Safiyar Asabar a gidan Makaman Fika a birnin Potiskum dake jihar Yobe kan sadaki dubu 50,000
Yan film da dama sun halarci taron bikin, daga ciki akwai Darakta Malam Aminu Saira, Aminu Unguwar Gini, Ahmed Bello, Sani Mai Iyali, Ahmad Nagudu da sauran su.
Muna yi musu addu'ar fatan alheri a wannan auren nasu, Allah ya basu Zaman lafiya da zuri'a dayyiba amin.
Allah ya basu zaman lafiya
ReplyDelete