Wata babbar kotun Musulunci a jihar Kano ta yanke wa Sheikh Abduljabbar Kabara hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan da kotun, ta same shi da laifin aikata kalaman rashin tarbiyya ga Annabi Muhammad SAW.
An yanke hukuncin ne a ranar Alhamis bayan da Mai Shari'a Ibrahim Sarki Yola ya ce an same da dukkan laifukan da ake tuhumarsa da su.
Daga cikin tuhumar da ake masa, hadda zargin wa'azinsa zai iya tayar da tarzoma a jihar Kano.
Bayan an same shi da laifukan, sai Mai Shari'a Sarki Yola ya dage zaman kotun don ba shi damar rubuta hukuncin da za a yanke wa malamin.
A bayaninsa na karshe kafin alkali ya yanke masa hukunci malamin ya yi bayani kamar haka;
''Ni bana neman sassauci akan wannan laifi da ban yi ba, ina bawa masoyana hakuri, kar su samu damuwa kan tafiya ta lahira, zanyi mutuwa ta girma, kuma bana neman kai Ibrahim Sarki Yola kayi mun sassauci, kuma a gaggauta yi mun hukuncin nan. Kalami na na karshe kenan.''
~Sheikh Abduljabbar Kabara